September 27, 2026

Hukumar hana fasa ƙwabri ta Najeriya ta cafke Bindigogi 140

0

Hukumar hana fasa ƙwabri ta Najeriya ta cafke Bindigogi 140

Daga Bashir Rabe Mani a Sokoto

Hukumar hana fasa ƙwabri ta Najeriya Customs ta cafke wata kontaina ɗauke da bindigogi 140 da wasu sinadaran Cannabis da kuɗin su ya kai miliyan 373.8 a tashar Jirgin ruwa ta Tincan dake Ikko.

Cikin wata sanarwar da Jami’in hulda da Jama’a na Hukumar Abdullahi Maiwada ya fitar ya ce sun gano kontainar ne bayan samun bayanan sirri da hakan ya taimaka wajen kame mutane biyu da ake zargi ya yin da ake ci gaba da neman sauran.

Shugaban Hukumar Adewale Adeniyi ya gargaɗi bata gari da suke amfani da kan iyakoki a lokacin zabe cewa za su ci gaba da ƙara ƙaimi wajen dakile ayyukan su.

Ya kuma buƙaci ƴan Nijeriya da su ci gaba da bada bayanan sirri wa hukumar don dakile ayyukan ƴan simogal a kan iyakokin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *