Gwamnan Jihar Sokoto Ahmed Aliyu Sokoto yayi gaisuwar ta’aziyyar wasu rashe-rashe da akayi a cikin babban birnin jiha
Gwamnan Jihar Sokoto Ahmed Aliyu Sokoto yayi gaisuwar ta’aziyyar wasu rashe-rashe da akayi a cikin babban birnin jiha

Daga Bashir Rabe Mani a Sokoto
Gwamnan Jihar Sokoto Ahmed Aliyu Sokoto, PhD, fcna ,yayi gaisuwar ta’aziyyar wasu rashe-rashe da akayi a cikin babban birnin jiha.
Gwamnan ya soma da unguwar Salame, inda yayi ta’aziyyar rasuwar Abubakar Mohammad mai shekaru 75 da ya rasu ya bar mata da ya’ya da dama.Sai kuma shiyar inguwar Mabera, inda gwamnan yayi gaisuwar rasuwar Hajiya zuwaira Abubakar,Daraktar Lafiya a yankin mulkin Dange Shuni, mai shekaru 65 data rasu ta bar ‘ya’ya 2,kazalika da kuma taaziyar marigayi Nasiru Ubale mai shekaru 65,da ya rasu ya bar mata 2 da ‘ya’ya 18 da jikoki da dama.
Haka zalika gwamnan yayi ta’aziyar rasuwar Aisha Bello Achida ,dake Unguwar Minanata ,da kuma gaisuwar rasuwar Hajiya Halima Mua’zu mai shekaru 75 dake unguwar Tudun wada,da Hajiya Rabi Kamaru Gada mai shekaru 60 da ta rasu ta bar ‘ya’ya 7.
Bugu da kari kuma,Gwamna Aliyu ya kai gaisuwar ta’ziyyar rasuwar Abubakar Raba mai unguwa dake shiyar maniru road,wanda ya rasu yana da shekaru 55,ya bar mata 2 da ‘ya’ya 6,kazalika da kuma ta’aziyar marigayi Nasiru PA na SA protocol dake shiyar Galadanci wanda Allah yayiwa cikawa kwanan nan.
Dukkan wuraren da Gwamnan ya yi Ta’aziyyar dai,yayi adduar neman gafara ga mamatan da kuma jajantawa ga iyalan su.
Abubakar Bawa
Darakta Janar,
Kula da yada labaru da hulda da yan jarida a fadar Gwamnatin jiha.
17/1/2027
