Gwamna Aliyu ya kai gaisuwar ta’aziya ga wadansu iyalai da suka rasa ‘yan uwansu a birnin Sakkwato

Gwamna Aliyu ya kai gaisuwar ta’aziya ga wadansu iyalai da suka rasa ‘yan uwansu a birnin Sakkwato

Daga Bashir Rabe Mani a Sakkwato
Gwamna Ahmad Aliyu Sokoto ya kai gaisuwar ta’aziyya ga wadansu iyalai da suka rasa yan uwansu a wasu unguwanni dake cikin babban birnin jiha
Daga cikin su akwai unguwar
kalambaina Bakin kusu inda yayi gaisuwar rasuwar marigayi Muhammadu Musa mai Shekaru 75,da ya rasu ya bar Mata 1 da ya’ya 11,sai kuma Unguwar takalmawa inda yayi ta’aziyyar rasuwar Alh. Arzika mai siminti mai shekaru 70 da ya rasu ya bar Mata 3 da ya’ya
30,sai kuma gaisuwar rasuwar
Zalihat Naibi Buhari Shehu na liman wadda Allah yayiwa cikawa da Shekaru 23 ta bar da daya.
Duk dai a yau,gwamnan yayi ta’aziyyar rasuwar Abdullahi Malami mai Shekaru 60 da ya rasu ya bar Mata 1 da ya’ya 6,da kuma gaisuwar Hajiya yar dubu yusuf Sahabi Asarakkawa mai shekaru 70 da ta rasu ta bar ya’ya 10.
A dukkan wuraren dai, Gwamnan ya bukaci iyalan dasu dauki rasuwar a matsayin wani hukunci daga Allah SWA, tare kuma da addu’ar Allah jikan mamatan.
Haka ma an gudanar da addu’oi na musamman don neman gafara ga mamatan a dukkan wuraren da Gwamnan ya ziyarta.
Abubakar Bawa
Darakta Janar Mai kula da yada Labarai da hulda da jama’a, a fadar gwamnatin jihar Sokoto.
8/10/2026
