September 27, 2026

GWAMNA AHMED ALIYU YA TALLAFAWA IYALIN WADANDA AKA KASHE DA WADANDA SUKA JIKKATA SANADIYAR HARIN YAN TA’ADDA A KEBBE

0
FB_IMG_1787586533251

GWAMNA AHMED ALIYU YA TALLAFAWA IYALIN WADANDA AKA KASHE DA WADANDA SUKA JIKKATA SANADIYAR HARIN YAN TA’ADDA A KEBBE

Daga Bashir Rabe Mani a Sokoto

Maigirma gwamnan Sokoto, Alhaji Dr. Ahmed Aliyu Sokoto, ya bayar da tallafin Naira miliyan 1 da buhunan abinci 5 ga iyalan kowanne mutum da aka kashe a hare haren da yan bindiga sunka kai a karamar hukumar Kebbe.

Haka kuma dukkanin wadanda suka samu raunuka maigirma gwamna ya basu tallafin kudi naira dubu dari biyu da hamsin (250,000) tareda basu buhuhuwan abinci uku ga kowanen su.

Maigirma Mataimakin gwamna Hon Dr Muhammad Idris Gobir shine ya wakilci maigirma gwamna tareda rakiyar sakataren gwamnatin jihar sokoto Hon Bello Sifawa, shugaban ma’aikata na fadar gwamnatin jihar sokoto Alh Aminu Dikko, mataimakin shugaban jam’iyar Apc na jiha Alh Yahya Buhari Siriddawa, Kwamishinoni, masu bada shawara da sauran mukarraban gwamnati

Yayin wannan ziyara shugaban karamar hukumar mulkin Kebbe Hon Musa Garba Kuchi yayi godiya ta musamman kan wannan ziyara jajantawa da aka kawoma al’ummar karamar hukumar mulkin Kebbe inda ya bayyana godiya su akan kokarin da gwamnatin jihar sokoto keyi na kara samun tsaro a jihar sokoto baki daya

Shuwagabannin al’umma wadanda suka hada da shuwagabannin siyasa, uwayen ƙasa, shuwagabannin jam’iyar Apc a mataki na karamar hukuma da mazabu, Malaman addini da sauran muhimman mutane na daga cikin wadanda suka shedi wannnan ziyarar ta’aziyyar wadda ta gudana a harabar fadar sarkin kebbin Kebbe dake garin Kebbe

Office of the Secretary, Kebbe Local Government Secretariat, Sokoto State
August. 24th, 2026

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *