September 27, 2026

Gwamna Ahmad Aliyu Sokoto ya kai gaisuwar ta’aziyya ga wadansu iiyalai a Birnin Sokoto-

0

Gwamna Ahmad Aliyu Sokoto ya kai gaisuwar ta’aziyya ga wadansu iiyalai a Birnin Sokoto-

Daga Bashir Rabe Mani a Sokoto

Gwamna Ahmad Aliyu Sokoto ya kai gaisuwar ta’aziyya ga wadansu iyalai da suka rasa ya unguwanni dake cikin babban birnin jiha

Daga cikin su akwai unguwar
Hausare ,inda yayi taaziyyar rasuwar Malam Bello Marafa,sai kuma unguwar Rungumi ,inda nan ma gwamnan yayi ta’aziyar rasuwar Mai unguwa Hamza
Babuga Alhaji,sai kuma Shiyar mabera, inda a can ma gwamna Ahmed Aliyu yayi taaziyar rasuwar Alhaji Sani Naguru wanda Allah yayiwa cikawa.

Haka ma, gwamnan ya ziyarci unguwar Tamaje, inda yayi ta’aziyar rasuwar Hauwau Abdullahi, wadda mahifiyace ga shugbar mata ta jamiyyar APC a yankin sokoto ta tsakiya,sai kuma a garin Tsehe,inda a can ma gwamnan yayi gaisuwar rasuwar marigayi Zubairu Alhaji shehu, kazalika da kuma gaisuwar rasuwar Hajiya Hauwau Zamau wadanda dukkanin su Allah yayi musu rasuwa.

Gwamna Aliyu ya kuma kai gaisuwar ta’aziyyar Abubakar Umar kyauta, mai shekaru 90 dake shiyar Mainiyo da ya rasu ya bar mata 1 da Ya’ya 11,da kuma yin ta’aziyyar rasuwar Aishatu Muhammed da Maryam Tambari da kuma malam Hassan na yar kaya dake unguwar gidan Haki.

A dukkan wuraren dai, Gwamnan ya bukaci iyalan dasu dauki rasuwar a matsayin wani hukunci daga Allah SWA, tare kuma da addu’ar Allah jikan mamatan.

Haka ma an gudanar da addu’oi na musamman don neman gafara ga mamatan a dukkan wuraren da Gwamnan ya ziyarta.

Abubakar Bawa
Darakta Janar Mai kula da yada Labarai da hulda da jama’a, a fadar gwamnatin jihar Sokoto.
15/08/2026

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *